Assalamu Alaikhum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuh
Barkanku da ziyartar shafin mu na Inganchi Development Foundation (IDF), wannam katafaren shafin an kafashi ne domin harkokin ilimi da kuma karantarwa ga dalibai musammn ‘yan secondary school masu niyyar zana jarabawar WAEC, NECO da JAMB. Wannan shafin ya samar muku da karantarwa wato (tutorials) ta hanyar video kuma ana yin bayani ne a takaice da HARSHEN HAUSA domin saukakama daliban mu ‘yan secondary fahimdar darussan turanci da kimiyya. Wannan aiki ayanzu ya shafi darussan English, Mathematics, Physics, Chemistry da kuma Biology. Har ila yau muna ta kokari domin kammala muku sauran darussan. Wanna shafin be tsaya anan ba domin ya tanaji tambayoyi (wato Past questions) na akalla shekaru goma domin wasa kwakwalwa da kuma samun tabbacin fahimtar karatuttuka. Wannan aikin yana gudana ne tare da tallafin wasu bayin Allah da kuma wasu manyan malaman mu na musulunci, sai kuma wasu jajirtattun dalibai ‘yan uwanku tare kuma da gudunmawar campanin Ruwaidah Ventures Limited wainda suka bamu mazauni na dindindin domin gudanar da wanna katafaren aiki. Dan bada gudun mawa, shawara ko kuma yi mana gyara, za’a iya samun mu a offishin mu da ke Block D Suit 1 & 2 Jigawa Shopping Complex Rabah Road Kaduna.